Isa ga babban shafi
Paris

An gudanar da zanga-zangar neman kubutar da al'ummar Uighur a Paris

A yau Asabar masu zanga zanga a birnin Paris  suka bukaci Tarayyar Turai ta haramta kayayyakin da ke da nasaba da ci da gumin ‘yan tsirarrun al’ummar Uighur da ke yankin Xinhjiang na kasar China.

Shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen.
Shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen. Patrick Hertzog Pool/AFP
Talla

Masu fafutuka da suka taru a dandalin Palace de la Republic a birnin Paris a Asabar, sun bukaci Tarayyar Turai ta dau mataki a game da take hakkin bil adama da ake yi wa al’ummar Uighur a lardin Xinjiang na arewa maso yammacin China.

Zanga zangar na zuwa ne makonni  bayan da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta sanar da shirin haramta shigowa da kayayyakin da aka samar da su ta wajen aikin dole.

A wata ganawa da tashar France24, Raphael Glucksman, dan majalisar Tarayyar Turai, ya zargi kamfanonin Turai da ke samun riba a kana bin da China ke yi da kokarin dakile matakin haramta kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin dole.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.