Isa ga babban shafi
China-Turai

EU za ta sanyawa China takunkumi kan azabtar da Musulmin Uighur

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da sanya takunkumi kan manyan jami’an gwamnatin China dangane da yadda kasar ke cin zarafi tare da kuntatawa tsirarun musulmi ‘yan kabilar Uighur.

Mata 'yan kabilar Uighur na fuskantar cin zarafin hana su haihuwa a Xianjing na China.
Mata 'yan kabilar Uighur na fuskantar cin zarafin hana su haihuwa a Xianjing na China. REUTERS/Petar Kujundzic
Talla

Kasashen na EU 27 sun aminta da matakin sanya takunkuman kan China saboda keta dokokin kare hakkin dan adam da ta ke ci gaba da yi kan tsirarun musulmi ‘yan kabilar Uighur baya ga azabtar da su.

A wani taron ministocin wajen kasashen 27 ranar Litinin mai zuwa ne takunkuman za su tabbata wadanda za su shafi hatta kasashen Rasha Korea ta Arewa da Eritrea da kuma Sudan ta Kudu baya ga Libya dukkaninsu saboda tuhume-tuhume ko kuma zargin take hakkin bil’adama.

Tuni dai China ta nuna bacin ranta game da yunkurin sanya mata takunkumai kan halin da ‘yan kabilar ta Uighur ke ciki a yankin Xinjiang inda jakadan kasar a EU Zhan Ming ke cewa Turai na shirin kakabawa Beijing takunkuman bisa kaffa hujja da kare-rayi baya ga rahotannin da basu da tushe.

A cewar Mr Zhan, China na bukatar tattaunawa ta fahimtar juna tsakaninta da EU amma kafin wannan yakamata Turai ta yi tunani sosai gabanin kakaba mata takunkuman wadanda za su shafi alakar da ke tsakaninsu, domin kuwa a acewarsa Beijing ba za ta zuba ido ba tare da daukar mataki ba.

Mr Zhan ya nanata cewa China ba ta da hannu a zargin da ake mata kuma a shirye ta ke ta mayar da martani kan duk wani yunkuri ko kuma barazana ga tsaro da manufofinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.