Faransa ta saida wa Girka karin jiragen yaki kirar Rafale
Ministar Tsaron Faransa Florence Parley ta ce Girka ta amince da sayen karin jiragen yakin da suke kerawa kirar Rafale guda 6.
Wallafawa ranar:
Yarjejeniyar cikinikin makaman ta sanya adadin jiragen yakin da Faransar ta saidawa Girka kaiwa 24 akan biliyoyin euro.
Girka ce dai kasar Turai ta farko da ta sayi jiragen yakin na Rafale daga Faransa, inda a watan Janairun da ya gabata, ta biya euro biliyan 2 da miliyan 500 akan jiragen guda 18, da zummar inganta karfin sojinta, sakamakon zaman tankiyar da ke tsakaninta da Turkiya.
A watan Mayu, Croatia ta zama kasa ta biyu ta Turai da ta sayi Rafales, inda ta zabi jirage 12 da aka yi amfani da su a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu