Jami'an kwana-kwana dubu 20 sun kasa kashe gobarar dajin California
Ma'aikatar gandun dajin Amurka ta ce mummunar gobarar dajin da ta tashi a sassan jihar California sama da kwanaki 30 da suka gabata, na ci gaba da kone fadin kasa mai yawan gaske, gami da barazanar lakume dubban gidaje a wasu karin yankuna da ke Yammacin kasar ta Amurka.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka dai jami’an kwana-kwana kusan dubu 21 sun gaza kashe gobarar dajin da kawo yanzu ta kone girman fadin kasar da ya kai murabba’in kilomita dubu 2, wanda ya zarce girman birnin London.
A Arewacin California kadai, kimanin ma’aikatan kashe gobara dubu 6 da 170 ke fafatawa da sashin wutar dajin mafi muni da masana suka yiwa lakabi da Dixie.
Yanzu haka dai kashe-kashen gobarar daji kimanin 100 ke ci a wasu sassan jihohi 14 da ke Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu