Isa ga babban shafi
BREXIT

EU ta yi watsi da bukatar Birtaniya na neman sabunta yarjejeniyar Brexit

Kungiyar kasashen Turai ta sa kafa ta shure sabuwar bukatar Gwamnatin Birtaniya na sabon tattaunawa game da cinikayya da Arewacin Ireland, bayan da aka sami dimbin hasara, yayin tarzoma da ya durkusar da harkokin kasuwanci a yankin.

Jiragen ruwan su na kasar Birtaniya
Jiragen ruwan su na kasar Birtaniya © FRED TANNEAU/AFP
Talla

Kasar Birtaniya na kusan jingine tsarin hulda da Arewacin Ireland ne, wanda ta gindaya a farkon wannan shekara, inda take bukatar sa idanu sosai kan kayayyakin dake shiga Birtaniya, inda take bukatar chanjin tsari.

Britaniya na bukatar Kungiyar Turai ta jingine dukkan matakan gaggawa na dan wani lokaci da aka kafa, don binciken kwakwaf akan iyakoki da kuma share batun matakin shara da aka kaddamar kan Britaniya saboda kin bin sharuddan da aka shimfida, duk dai don a sake sabon zubi.

Sakataren yankin na Northern Ireland Brandon Lewis ya fadi cewa bayan da Britaniya ta tsara wancan yarjejeniya, da kyakkyawan nufi akwai matsala sosai wajen aiwatar da tsarin.

Ya shaidawa majalisar Britaniya cewa sam ba za su iya aiki da tsarin ba, inda yake fatan kungiyar Turai za ta dube su da idon basira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.