Isa ga babban shafi
Turai-Birtaniya

Turai ta amince da yarjejeniyar kasuwancin Birtaniya

Majalisar Dokokin Turai ta amince da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin EU da Birtaniya, sai dai majalisar ta ce za ta sanya idanu kwarai kan yadda Birtaniyar za ta tafiyar da wannan sabuwar yarjejeniya.

Tutocin Birtaniya da Turai
Tutocin Birtaniya da Turai Olivier HOSLET POOL/AFP/File
Talla

Mafi rinjayen mambobin majalisar ne suka kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar a yau Laraba, wadda za ta zama yarjejniyar kasuwanci ta uku mafi girma a duniya.

Yarjejeniyar ta kunshi amincewa da yadda a yanzu Birtaniya za ta rika mu’amalantar kasashe mamboboin tarayyar Turan 27, shekara guda bayan da kasar ta fice daga EU bayan shafe tsahon shekaru 47 a cikin ta.

Wannan ita ce yarjejeniya irinta ta uku da tarayyar Turai ta shiga da wata kasa tun bayan kasashen China da Amurka da kuma Switzerland kamar yadda shugaban majalisar David Sassoli ya tabbatar.

A cewar Mr. David wannan zai zama wata hanya ta kara kulla alaka tsakanin EU da Birtaniya, kasancewar tun bayan ficewarta babu wata alakar diflomasiyya da ta shiga tsakaninsu.

Tuni Birtaniya ta bakin Firaminista Boris Johnson ta yaba da matakin majalisar na amincewa da yarjejeniyar, yana mai cewa hakan zai kara inganta alaka a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.