Isa ga babban shafi
Colombia

An bude wa jirgin saman da shugaban Colombia ya ke ciki wuta

Shugaban Colombia, Ivan Duque ya ce an harbi jirgi mai saukar ungulyu da yake ciki a jiya Juma’a, kusa da iyakar Venezuela, a hari na farko da aka kai wa wani shugaban kasar a cikin shekaru 20.

Hotunan da shugaban Colombia Ivan Duque ya wallafa da ke nuna alamun harbin bindiga a jikin jirgi mai saukar ungulu da yake ciki.
Hotunan da shugaban Colombia Ivan Duque ya wallafa da ke nuna alamun harbin bindiga a jikin jirgi mai saukar ungulu da yake ciki. - Colombian Presidency/AFP
Talla

Babu wanda ya samu rauni a  wannan harin, kuma hukumomi ba su bayyana ko daga ina ne harin ya taho ba.

Dama Colombia ta sha zargin Venezuela da bai wa ‘yan tawayen kasarta mafaka.

Duque ya ce yana tafiya ne tare da ministan tsaro da na cikin gida da kuma gwamnan lardin  Norte de Satanda, wanda ke iyaka da Venezuela, kwatsam sai ga harbi.

 Hotunan da fadar shugaban kasar ta saki na nuni da yadda harsasai suka huda wutsiya da farfelar jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.