Isa ga babban shafi
Jamus - Namibia

Jamus ta amince da aikata kisan kiyashi a Namibia a lokacin mulkin mallaka

Kwana daya bayan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da kuskuren da kasarsa ta tafka a kisan kiyashin Rwanda, a karon farko kasar Jamus ta amince da aikata kisan kare dangi a Namibia a lokacin mulkin mallaka, inda ta yi alkawarin ba da tallafin kudi na sama da Euro biliyan daya a matsayin diyya ga kasar dake Kudancin Afirka.

Turawan mulkin mallakar Jamus sun aikata kisan kiyashi a Namibia masamman kibilun Herero da Nama a shekarun 1904-1908
Turawan mulkin mallakar Jamus sun aikata kisan kiyashi a Namibia masamman kibilun Herero da Nama a shekarun 1904-1908 John MACDOUGALL AFP
Talla

Turawan mulkin mallaka na Jamus sun kashe dubun dubatan kabilun ‘yan asalin Herero da Nama a wani kisan gillar da aka yi a shekarun 1904-1908 - wanda masana tarihi sukayi wa lakabi da kisan kare dangi na farko a karni na 20 da ya lalata dangantaka tsakanin Namibia da Jamus tsawon shekaru.

Duk da yake Berlin ta amince da lallai da sa hannun mahukuntar mulkin mallaka a ta'asar ta Namibiya, ta dage kan kin daukar alhaki kai tsaye da kuma watsi da butun biyan kudin diyya.

Amincewa karon farko

To sai dai cikin sanarwa da ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maas ya fitar ranar Jumma’a ya ce "Yanzu sun amince tare da ambatan Kalmar kissan kare dangi a hukumance.

Inda ya yaba da yarjejeniyar fahimtar juna da suka samu bayan kwashe sama da shekaru biyar suna tattaunawa da Namibia kan abubuwan da suka faru a yankin da Berlin ta rike daga shekarun 1884 zuwa 1915.

"Dangane wannan nauyi da tarihi ya nuna, da irin ɗabi'a na Jamus, za mu nemi gafara daga Namibia da zuriyar waɗanda aka cutar" don "ta'asar" da aka aikata, in ji Maas.

Biyan diyya

Ministan yace, domin nuna karamci jamus zata tallafawa Nabiya  da Euro biliyan daya da miliyan 100 don sake ginata da ci gaban kasar.

Majiyar kusa ta yarjejeniyar tace, cikin shekaru 30 Jamus zata biya kudin sannu a hankali, kuma dole ya soma da zuriyar Hereo da Nama kai tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.