Isa ga babban shafi
Rwanda-Faransa

Macron ya amince da sakacin Faransa kan dakile kisan kiyashin Rwanda

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince kasar sa ta taka rawa a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda cikin shekarar 1994.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Kigali babban birnin kasar Rwanda. 27/5/2021.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Kigali babban birnin kasar Rwanda. 27/5/2021. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Macron ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar a Kigali babban birnin Rwanda, yayin taron alhinin tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa mutane akalla dubu 800 a kasar, mafi akasrinsu ‘yan kabilar Tutsi.

Yayin jawabin nasa, shugaban ya ce wadanda suka tsira daga tashin hankalin kisan kiyashin kuma suke raye ne kawai za su iya taimakawa wajen yafewa Faransa laifin da ta aikata musu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa ba Rwanda Paul Kagame a fadar gwamnatin kasar dake birnin Kigali. 27/5/2021.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa ba Rwanda Paul Kagame a fadar gwamnatin kasar dake birnin Kigali. 27/5/2021. AFP - LUDOVIC MARIN

Emmanuel Macron shi ne shugaban Faransa na farko tun shekarar 2010 da ya ziyarci Rwanda, kasar da ta share shekaru tana tuhumar Faransar da bayar da gudunmawa wajen kisan kiyashin da aka yi a 1994 yayin rikicin kabilanci mafi muni da aka gani a kasar.

Karo na farko kenan da wani shugaban Faransa ya amince da laifin kasar na yin watsi da gargadin masana kan barazanar dubban jama’a ke fuskanta a Rwanda na yi musu kisan kiyashi, da kuma goyon bayan gwamnatin mulkin kama karya da Faransar tayi da gangan a waccan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.