Isa ga babban shafi
Namibia

Namibia za ta saida giwaye 170 don takaita hauhawar adadinsu

Gwamnatin Namibia ta sanar da shirinta na sayar da giwaye 170 domin wasu dalilai, ciki har da manufar rage yawansu dake karuwa cikin sauri, musamman nau’ikan giwayen masu girman hauren da ke jan hankalin masu safarar hauren ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin Namibia ta sha alwashin takaita adadin giwayen dake kasar
Gwamnatin Namibia ta sha alwashin takaita adadin giwayen dake kasar Reuters
Talla

Sauran dalilan da suka sanya gwamnatin Namibian yanke shawarar saida giwayen kusan 200 sun hada da barazanar da suke fuskanta daga iftila’in fari a sassan kasar, gami da karin barzanar da suke fuskanta daga mutane dangane da sarari.

A ranar Laraba ne dai jaridar ‘New Era’ mallakin gwamnatin kasar Namibian ta wallafa tallar saida giwayen 170, matakin da ministan muhallin kasar ya ce gwamnati ta dauka bayan watsi da tsarin kashe dabbobin don takaita hayayyafar da suke, abinda a baya ya janyo musu caccaka a ciki da wajen kasar.

Yanzu haka dai adadin giwayen da ke kasar Namibian ya kai akalla dubu 28, idan aka kwatanta da shekarar 1990 da kasar ta samu ‘yancin kai, lokacin adadinsu bai wuce dubu 5 ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnatin Namibia ke saida dabbobin dawa masu rai ba, domin ko a watan Oktoban da ya gabata ta saida Bauna 100, yayinda a shekarar bara ta sanya kimanin dubu 1000 a kasuwa da suka hada da Bauna 600, giwaye 28 da kuma rakuman dawa 60.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.