Isa ga babban shafi
Afrika

Afrika ta rasa wanda zai lashe kyautar Dala miliyan 5

Shekaru biyu kenan a jere da aka rasa wani shugaba daga nahiyar Afrika da ya cancanci lashe kyautar Dala Miliyan 5 da gidauniyar Mo Ibrahim ke bai wa shugaban da ya fi fice musamman ta fannin mutunta demokradiya.

Gidauniyar Mo Ibrahim na bai wa shugaban Afrika da ya fi yin fice wajen mutunta demokradiya kyuatar Dala miliyan 5
Gidauniyar Mo Ibrahim na bai wa shugaban Afrika da ya fi yin fice wajen mutunta demokradiya kyuatar Dala miliyan 5 Mo Ibrahim Foundation
Talla

Tun bayan kafa wannan gidauniya a shekara 2006, shugabanni Afrika hudu kadai ne suka lashe kyutar ta Dala miliyan 5 da suka hada da Joacquim Chissano na Mozambique da Festus Mogae na Botswana da Pedro De Verona Rodrigues Pires na Cape Verde, da kuma Hifikepunye Pohamba na Namibia wanda ya lashe a shekarar 2014.

Gabanin samun wannan kyauta dai, dole ne shugaba daga Afrika ya zamanto cewa an zabe shi ne ta hanyar demokradiya, sannan aka samu tazarar shekaru uku da saukarsa daga kujerar mulki.

To sai dai ana ci gaba da samun karancin shugabanni na Afrika da suka cika wadannan sharuddan.

Kana koda kuwa shugaba ya mika mulki cikin ruwan sanyi amma aka zarge shi da laifin wawure dukiyar takalawa, to lallai babu yadda za a yi ya lashe wannan kyauta ta MO Ibrahim.

Shugaban kwamitin bada kyautar, Salim Ahmed Salim ya ce, makasudin bada kyautar shi ne yaba wa jagoranci na gari a nahiyar Afrika.

Baya ga Dala Miliyan 5, har ila yau gidauniyar za ta ci gaba da bai wa shugaban da ya yi nasara Dala dubu 200 a matsayin fansho duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.