Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka na daf da komawa yarjejeniyar nukiliyar Iran

Bangarorin da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran sun tashi daga zagaye na 3 na taron da suke don maido da Amurka cikin yarjejeniyar a jiya Asabar, inda ma Rasha ke bayana kwarin gwiwar cewar za  a cimma gaci nan da makonni 3 masu zuwa.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. Melina Mara POOL/AFP
Talla

Wata majiyar diflomasiyya daga manyan kasashen da ke cikin yarjejeniyar t ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa ba  akai ga fahimtar juna a game da mahimman batutuwa ba, amma babu abin da zai gagara.

Jagoran tawagar Iran a taron , kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar ta kai wani mahimmin mataki.

Yarjejeniyar nukiliyar Iran na cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai tun  bayan da tsohon  shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga cikinta a shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.