Isa ga babban shafi
Somalia

'Yan adawa sun bijire wa shugaban kasar Somalia da ke neman zarcewa

Rikici na shirin kunno kai a Somalia, bayan da ‘yan adawa suka bijere wa bukatar Shugaban kasar, wanda wa’adin mulkin sa ya kawo karshe a jiya Lahadi ya nemi samun goyon bayan wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a siyasar kasar.

Shugaban Somalia, Mohamed Abdullahi Mohamed.
Shugaban Somalia, Mohamed Abdullahi Mohamed. AFP
Talla

Kasar Samalia na dada fadawa cikin rikicin siyasa, a wani lokaci da ‘yan adawa ke ci gaba da bayyana adawar su ga zabin shugaban kasar, tare da bayyana shugaban a matsayin haramtacen shugaban, ‘yan sa’o’i da kawo karshen wa’adin mulkinsa Lahadi, 07 ga wannan watan da muke cikin sa.

Daga Litinin, hadakar jam’iyoyin adawa sun bayyana shugaban kasar Farmajo a matsayin haramtace, wanda ba za su amince da duk wani shiri na ba shi damar ci gaba da mulkin kasar .

Ranar 17 ga watan Satumba na shekara da ta shude ne Shugaban kasar Mohamed Abdullahi Mohamed da ake yi masa inkiya na Farmajo ya cimma wata ‘yar gajeruwar yarjejeniya da wasu shugabanin yankunan kasar biyar hade da magajin garin Mogadisho da zummar shirya zaben kasar ranar 8 ga watan Fabrairu shekarar bana.

Wannan yarjejeniya na kawo karshen zaman sulhu da aka cimma tare da shirya.

‘Yan adawa na kira ga shugaban kasar ya mutunta dokokin kasar tare da kafa wani kwamitin wucin - gadi na musaman da za su yi aiki da wakilan jama’a a majalisa, shugabanin al’umma da wasu wakilan kungiyoyin farraren hula da nufin shirya zaben kasar.

A karshe Majalisar Dinkin Duniya, Amurka, kungiyar tarrayar Turai, rundunar sojin Afrika dake aiki a kasar a karkashin kungiyar Amisom, da wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana damuwa a wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka bukaci ‘yan siyasar kasar sun cimma matsaya ta sulhu don ceto kasar ta Somalia daga tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.