Isa ga babban shafi
Somalia

Somalia ta bayyana mamayar farin dango a matsayin annoba

Gwamnatin Somalia ta yi shelar bayyana mamayar da farin dango ke yiwa gonaki da rumbunan abinci a kasar da wasu sassan yankin gabashin Afrika a matsayin annoba.

Wani manomi yayin kokarin korar farin dango daga gonarsa a garin Jijiga dake lardin Somali a kasar Habasha.
Wani manomi yayin kokarin korar farin dango daga gonarsa a garin Jijiga dake lardin Somali a kasar Habasha. REUTERS
Talla

A karshen watan Janairun da ya gabata hukumar samar da abinci da bunkasa ayyukan noma ta majalisar dinkin duniya FAO ta bayyana kawararar fadin dangon kan Somalia a matsayin mafi muni cikin shekaru 25.

Hukumar ta FAO ta kuma ce hadarin farin dangon da ya taso daga Habasha da Somalia zuwa Kenya, ya kai girman murabba’in kilomita dubu 2 da 400, kwatankwacin girman birnin Moscow, abinda ke nufin adadin farin zai iya kaiwa biliyan 200.

Masana dai sun yi gargadin cewar, biliyoyin farin dangon dake afkawa gonaki da rumbunan abinci a sassan gabashin Afrika, na da nasaba da sauyin yanayi.

Wata kididdiga da cibiyar lura da wadatar abinci ta gabashin Afrika ta nuna cewar, sama da mutane miliyan 19 yanzu haka ke fuskantar bala’in yunwa, saboda matsalar karancin abincin da yayiwa yankin katutu tsawon lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.