Isa ga babban shafi
Somalia

Majalisar Somalia ta tsige firaminista

Majalisar Dokokin kasar Somalia ta tube Firaminista Hassan Ali Khaire daga mukamin sa bayan ta kada kuri’ar rashin amincewa da jagorancinsa saboda gazawa wajen daukar matakan tsaro.

Firaministan Somalia Hassan Ali Khaire.
Firaministan Somalia Hassan Ali Khaire. REUTERS/Feisal Omar/File Photo
Talla

Shugaban Majalisar Dokokin Mohammed Mursal Sheikh Abdirahman ya sanar da daukar matakin wanda ya samu goyan bayan Yan Majalisu 170, yayin da 8 kawai suka ki amincewa da shirin.

Rahotanni sun kuma ce daukar matakin na da nasaba da takun sakar da ake tsakanin shugaban kasa Mohammed Abdullahi Mohammed da Firaminista Khaire da kuma shugabannin Yankunan kasar kan cigaba da shirin gudanar da zaben da aka tsara a watan Fabararirun shekarar 2021.

Shugaban Majalisar dokokin yace Firaminista Khaire ya gaza wajen kafa rundunonin tsaron da zasu tabbatar da tsaro a matakin Jihohi da kuma tarayya.

Shugaban kasa Mohammed ya sanar ta gidan rediyo cewar ya amince da matakin da Yan Majalisun suka dauka, kuma nan bada dadewa ba zai nada wani sabo da zai maye gurbin Khaire da aka tsige.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.