Isa ga babban shafi
Amurka

Kamfanin Twitter ya rufe shafin Donald Trump

Kamfanin Twitter ya sanar da rufe shafin da shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ke amfani da shi, matakin da yace na dindindin ne, domin gudun kada shugaban ya sake amfani da shafinsa wajen tunzura magoya bayansa domin tayar da hatsaniya kamar yadda suka yi ranar Laraba a zauren majalisar dattijan kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump AP Photo/Julio Cortez
Talla

Matakin Twitter na rufe shafin Trump da akalla mutane miliyan 88 ke bibiya, na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki kalilan ya mikawa zababben shugaba Joe Biden mulki.

Karo na farko kenan da kamfanin Twitter ya rufe shafin da wani shugaban kasa ke amfani da shi.

Trump dai ya dade yana amfani da shafinsa na Twitter dama wasu kafafen, wajen ikirarin an tafka magudi a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba da ya sha kaye a hannun Joe Biden, inda a ranar Laraba ya bukaci magoya bayansa su yi tattaki zuwa majalisar dattijan kasar don gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaben, lamarin da ya kai ga mutuwar akalla mutane 5, sakamakon hatsaniyar da ta dakatar da zaman majalisar babu shiri don neman tsira da rai.

A makon da ya kare shi ma kamfanin sada zumunta na Facebook ya sanar da aniyarsa ta rufe dandalin da shugaban na Amurka mai barin gado ke amfani da shi da zarar ya mikawa Joe Biden mulki a ranar 20 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.