EU ta agaza wa 'yan gudun hijirar Bosnia
Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da bada karin tallafin agaza wa ‘yan gudin hijirar Bosnia da ke cikin mawuyacin hali, amma ta bukaci gwamnatin kasar da ta sake gina wa ‘yan gudun hijirar sansaninsu da gobara ta cinye.
Wallafawa ranar:
Kungiyar Tarrayar Turai ta yi tur da halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki a Bosnia, tana mai gargadin cewa, rayuwarsu na fuskantar barazana.
A ranar 23 ga watan Disamban bara ne gobara ta cinye sansanin ‘yan gudun hijira na Lipa da ke yankin arewa maso gabashin Bosnia , amma babu wanda ya rasa ransa a sanadiyar ibtila’in, illa lalata rumfuna da ta yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu