Isa ga babban shafi
Faransa

Masu shigar da kara sun bukaci daurin shekaru 4 kan Sarkozy

Masu gabatar da kara a Faransa sun bukaci kotu ta daure tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy shekaru 4 a gidan yari saboda samun sa da laifin yunkurin bai wa alkali cin hanci domin samun bayanai daga wurinsa.

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy Yoan Valat/Pool via REUTERS
Talla

Bukatar daure tsohon shugaban kasar ta biyo bayan zargin da ake masa na yunkurin bai wa alkalin cin hanci domin samun bayanan binciken da ake kansa na karbar kudade daga hannun tsohon shugaban Libya Muammar Ghadafi domin yakin neman zabensa a shekarar 2007.

Masu gabatar da karar sun nemi daurin shekaru 4 a gidan yari kan Sarkozy, inda zai yi shekaru 2 na daurin talala, yayin da shi ma lauyansa Thierry Herzog zai fuskanci irin wannan hukunci tare da alkalin mai suna Gilbert Azibert.

Lauyoyin sun kuma bukaci hana Herzog aikin lauya na tsawon shekaru 5 saboda laifin da ya aikata.

Sarkozy wanda ya jagoranci Faransa tsakanin shekarar 2007 zuwa 2012 ya shaida wa kotun cewar shi bai aikata wani laifi ba, kuma zai ci gaba da fafutukar kare kansa.

Ita dai wannan shari’a ta cin hanci da kuma yunkurin kawar da shaidu na dauke da hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari da tarar kudin da ya kai euro miliyan guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.