Isa ga babban shafi
Faransa

An tura 'yan sandan Faransa da sukaci zarafin Bakar fata kurkuku

Masu gabatar da kara a birnin Paris na Faransa sun bukaci a ci gaba da tsare 3 daga cikin ‘yan sanda 4 da wani hoton bidiyo ya nuna suna lakadawa wani Froduzan waka bakar fata dukan tsiya, lamarin da ya haifar da muhara a kasar.

Yan sandan Faransa
Yan sandan Faransa Eric Gaillard/Pool via AP
Talla

Ranar Lahadi babban mai gabatar da kara Remy Heitz ya gurfanar da ‘yan sandan, inda ya tuhume su da laifin cin zarafin bil adama, da nuna wariya tare da bukatar ci gaba da tsare uku daga cikin su, da kuma bukatan daukar kwakwaran mataki kan dan sanda na hudun.

Wannan mataki na zuwa ne bayan kazamnin zanga-zangar da akayi a fadin kasar domin nuna adawa da sabuwar dokar tsaron kasar da ke haramta daukar ‘yan sanda hoto yayin gudanar da aikinsu, wanda masu sukar dokar ke ganin shirye-shiryen shugaba Macron ne na hana ‘yan jaridu gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin zai bayyana gaban majalisar dokokin kasar domin amsa tambayoyin kwamitin Majalisar dangane da sabuwar dokar tsaron dake haramta daukar hoto ko wallafa shi na ‘yan sanda dake gudanar da ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.