Isa ga babban shafi
Faransa

An gudanar da zanga-zangar adawa da dokar hana daukar 'yan sandan Faransa hoto

'Yan Sanda a Paris dake Faransa sun yi arangama da dubban mutanen da suka shiga zanga zangar adawa da wata doka da ake shirin yi wadda zata hana jama’a wallafa hotunan jami'an nasu a lokacin da suke gudanar da ayyukan su.

Masu zanga-zangar adawa da dokar hana daukar yan sanda hoto yayin aikinsu
Masu zanga-zangar adawa da dokar hana daukar yan sanda hoto yayin aikinsu REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

Rahotanni sun ce an gudanar da zanga zangar a fadin kasar baki daya, inda a birnin Paris kawai akayi kiyasin cewar mutane sama da 46,000 suka shiga jerin gwanin wanda ya gamu da cinna wuta da harba hayaki mai sa hawaye.

Hoton bidiyon da aka yada na Yan Sandan na dukar wani mai shirya wakoki Michel Zickler ya haifar da suka mai zafi kan jami’an, ciki harda shugaba Emmanuel Macron wanda ya bayyana shi a matsayin abin kunya a gare su.

Masu zanga zangar na dauke da rubuce rubucen dake nuna cewar, ‘Yan Sanda a ko ina, amma kuma babu adalchi’, da ‘kasar kama karya’ da ‘kayi murmushi idan ana dukan ka’ lokacin da suka yi tattaki zuwa Dandalin ‘yanci.

Mohammed Magassa dake aiki cibiyar kula da yara yace jami’an tsaron na take hakkin dimokiradiya da kuma zamantakewar kasar.

Wasu masu zanga zangar sun yi ta jifar Yan Sandan da duwatsu, yayin da aka cinnawa motoci da shaguna wuta.

Rahotanni sun ce an gudanar da irin wannan zanga zangar a biranen Bordeaux da Lille da Montpellier da kuma Nantes.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.