Isa ga babban shafi
Faransa

Masu lalata muhalli zasu sha daurin shekaru 10 a Faransa

Gwamnatin Faransa ta bayyana shirinta na daurin shekaru 10 a gidan yari ga masu lalata muhalli da gangan.

Zanga-zangar adawa da manafofin gwamnatin India kan gurbatar yanayi
Zanga-zangar adawa da manafofin gwamnatin India kan gurbatar yanayi AP Photo/Manish Swarup
Talla

Ministocin gwamnatin Faransa sun ce, wannan mataki wani bangare ne na dokar yaki da masu yi wa muhalli illa.

Ministan shari’ar Faransa, Eric Dupont-Moretti da takwararsa ta kare alakar halittu da muhalli, wato Barbara Pompili sun ce, za a ci tarar masu sakacin lalata muhallin har Euro miliyan 4.5 ko kuma zaman gidan yarin shekaru 10.

Dupont Moretti ya ce, za su samar da dunkulalliyar dokar yaki da gurbata muhalli kuma za a hukunta mutane daidai da girman barnar da suka yi wa muhallin a Faransa.

Kodayake kundin tsarin mulkin Faransa bai bada damar daukar masu gurbata muhalli a matsayin masu aikata miyagiun laifuka ba, kamar yadda Ministan Shari’ar ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan wata Kungiyar Rajin Kare Muhalli wadda gwanmati ta kafa shekara guda da ta gabata, ta bada shawarar kafa dokar muhallin bayan ta tafka muhawara da mutane 150 da suka wakilci bangarori da dama na al’ummar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.