Masu cin zarafin dabbobi zasu sha daurin shekaru 10 a Girka
Majalisar Dokokin Girka ta kada kuri’ar amincewa da wata doka wadda zata bada damar daure mutanen dake cin zarafin dabbobi shekaru 10 a gidan yari, a wani yunkuri na kawo karshen yadda ake zin zarafin su.
Wallafawa ranar:
Dokar ta bayyana cewar masu aikata laifin kuma zasu biya tarar tsakanin euro 5,000 zuwa 15,000 muddin aka gan su suna sanya dabobi guba ko rataye su ko kona su da ran su ko kuma cire wani sashe na jikin su.
Ministan dake kula da ayyukan noma Makis Voridis da ya gabatar da kudirin yace yadda Majalisar dokokin ta amince da dokar da gagarumin rinjaye zai aike da sako mai karfi ga jama’ar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu