Isa ga babban shafi
Turai

Coronavirus ta halaka mutane 889 a Italiya, 319 a Faransa cikin kwana 1

Yawan wadanda annobar ta coronavirus ta halaka a yau asabar kadai a Italiya ya kai 889, abinda ya sanya jimillar adadin mutanen da cutar ta aika lahira a kasar haura dubu 10.

Wasu jami'an lafiya a nahiyar Turai.
Wasu jami'an lafiya a nahiyar Turai. SEBASTIEN BOZON / AFP
Talla

Bayan halaka jimillar mutane dubu 10 da 23, yanzu haka yawan wadanda annobar murar ta shafa a Italiyan ya kai dubu 92 da 427, bayan samun karin mutane dubu 5 da 900 da 74, tun bayan bullar annobar cikin kasar a watan fabarairu.

A Faransa kuma, ma'aikatar lafiyar kasar ta ce a yau asabar kadai mutane 319 annobar murar coronavirus ta halaka, abinda ya sanya jimillar wadanda suka rasa rayukansu tun bayan bullar annobar a kasar kaiwa dubu 2 da 314.

A bangaren wadanda suka kamu da cutar kuma, a yanzu haka jimillar mutane dubu 37 da 575 ne annobar ta shafa a fadin kasar ta Faransa, bayan samun karin mutane dubu 4 da 611 da suka kamu a yau asabar kadai.

Sai dai wasu majiyoyi sun ce adadin wadanda annobar murar ta halaka gami da shafa, ka iya zarta alkalumman gwamnati, la’akari da cewar ana maida hankali ne wajen kididdigar wadanda suka mutu a asibiti kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.