Isa ga babban shafi

Kashi 1/3 na al’ummar duniya ke zaman gida na tilas

Kashi daya bisa uku na al’ummar duniya yanzu haka suke zaman gida na tilas sakamakon wannan annoba ta coronavirus ko kuma COVID-19 dake cigaba da hallaka rayuka bayan ta ratsa kasashen duniya 175.

Yadda aka toshe hanyoyi a kasar Indiya don hana fita, domin yaki da yaduwar cutar coronavirus
Yadda aka toshe hanyoyi a kasar Indiya don hana fita, domin yaki da yaduwar cutar coronavirus Jewel SAMAD / AFP
Talla

Kasashe 42 suka kafa dokan hana fita na dole domin rage yaduwar cutar cikin su harda Birtaniya da Faransa da Italiya da Spain da Colombia da Amurka da Nepal da Iraqi da kuma Madagaska.

Kasashen baya-bayan nan da suka sanya dokar hana fitar harda kasashen New Zealand da Africa ta Kudu.

Kasar India mai dauke da mutane sama da biliyan guda ma, ta bi sahun kasashen da suka sanya wannan doka, inda Firaminista Narendra Modi ya bukaci al'umma su zauna a gida na makwanni 3.

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, Modi yace domin kare kowanne dan kasa da iyalan su, ya zama dole a rufe kowanne titi da unguwanni da kuma garuruwa.

Alkaluma sun nuna cewar mutane sama da biliyan 2 da rabi dokar hana fita ta shafa a kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.