Isa ga babban shafi
Faransa

Coronavirus ta halaka Faransawa 108 a kwana daya

Ma’aikatar lafiyar Faransa ta ce annobar murar Coronavirus ta halaka mutane 108 a kasar cikin kwana daya, adadi mafi muni tun bayan bullar da cutar tayi a kasar, bayan yaduwa daga China, gami da zamewa duniya annoba.

Jami'an lafiya a gabashin kasar Faransa, bayan dauko daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar murar Coronavirus. 17/3/2020.
Jami'an lafiya a gabashin kasar Faransa, bayan dauko daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar murar Coronavirus. 17/3/2020. AFP
Talla

Yanzu haka dai jimillar adadin mutanen da annobar ta kashe a Faransa ya kai 372.

Alkalumma dai na nuni da cewa karfin yaduwar annobar karuwa yake a Faransa da sauran sassan nahiyar Turai musamman a Italiya inda lamarin ya fi muni, sai kuma Iran a yankin gabas ta tsakiya, inda annobar ta halaka mutane 149 a kwana daya.

A ranar laraba dai mutane 89 annobar murar ta Coronavirus ta halaka a Faransa.

Alakalumman baya bayan nan da hukumomin lafiya suka fitar sun nuna cewar idan aka dauke Italiya, kasashen Spain da Faransa ke kan gaba wajen fama da annobar murar ta Coronavirus a Turai, nahiyar da majalisar dinkin duniya ta bayyana a matsayin sabuwar cibiyar annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.