Isa ga babban shafi

EU na duba yiwuwar sake karawa Birtaniya wa'adin Brexit

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun ce suna duba bukatar da Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sake shigarwa gabansu na tsawaitawa kasar lokacin ficewa daga Tarayyar Turai, bukatar da ‘yan Majalisun kasar suka tirsasa masa mikawa bayan zama na musamman a jiya asabar kan sabuwar yarjejeniyar da ya yi nasarar cimmawa da kungiyar ta EU.

Majalisar Birtaniya lokacin da ta ke kada kuri'a kan kudirin sake neman tsawaita wa'adin ficewar kasar daga Turai a ranar Asabar 19 ga watan Oktoba.
Majalisar Birtaniya lokacin da ta ke kada kuri'a kan kudirin sake neman tsawaita wa'adin ficewar kasar daga Turai a ranar Asabar 19 ga watan Oktoba. Parliament TV via REUTERS
Talla

Yayin zaman majalisar Birtaniyar na jiya, ‘yan majalisan sun ki amincewa da mara baya ga sabuwar yarjejeniyar ta Johnson matakin da ya kalubalanci kudirinsa na ganin lallao kasar ta kammala ficewa nan da ranar 31 ga watan nan.

A zaman na jiya wanda ke matsayin na tarihi ga kasar Birtaniya wadda bisa tsari ba ta gudanar da zama a ranakun karshen mako, ‘yan Majalisar sun caccaki yarjejeniyar ta Johnson wadda ya yi nasarar kulla da Brussels a makon jiya.

Maimakon amincewa da sabuwar yarjejeniyar ta Johnson majalisar ta Birtaniya ta kada kuri’ar samar da wani kudiri wanda ya bukaci shugaban ya nemarwa kasar karin wa’adin ficewa maimakon 31 ga watan Oktoba.

Shugaban na Jam’iyyar Conservative Boris Johnson wanda a baya ya kafe kan lallai kasar ta kammala ficewa daga EU ko da babu yarjejeniya a karshen wannan wata nan, tuni ya aikewa EU wata wasikar gaggawa da ke neman karin wa’adin watanni 3 gabanin ficewar ko da dai bai sanyawa wasikar hannu ba.

Cikin wasikar Johnson ya ja hankali kan illar da sake tsawaita wa'adin kan ficewar Birtaniya zai haifarwa kasar dama sauran abokananta kasashen Tarayyar Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.