Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Macron na yunkurin lalubo mafita game da rikicin Amurka da Iran

Fadar gwamnatin Faransa ta ce shugaba Emmanuel Macron ya aike da babban mai ba shi shawara ta fanni diflomasiyya Iran, a wani yunkurin Turai na lalubo mafita game da zaman tankiya da ake tsakanin Amurka da Iran din. 

Shugana Faransa, Emmanuel Macron
Shugana Faransa, Emmanuel Macron Ian Langsdon/Pool via REUTERS
Talla

Tuni ma babban jami’in diflomasiyyan na shugaba Macron, Emmanuel Bonne, ya isa Tehran har ma ya gana da manyan jami’ai da zummar kwantar da hankula game da rikicin da ke daf da kunno kai, sai dai fadar shugaban na Faransa ba ta bayyana wadanda Bonne ya gana da su ba.

Rikici tsakanin Amurka da Iran ya dada rincabewa a yau Alhamis, bayan sanarwa da rundunar sojin kare juyin – juye – hali na Iran ta fitar na cewa ta harbo jirgin Amurka maras matuki da ya ratsa sararin samaniyar ta ba tare da izini ba.

Wannan lamari da ya sake daga hankula a baya- bayan nan na zuwa ne mako daya bayan wani hari da aka kaiwa wasu tankunan mai a tekun Oman, aika aikan da Amurka ke nuna wa iran yatsa akai.

Macron, wanda zai halarci taron koli na G20 da zai gudana a Osaka na Japan daga ranar 28 zuwa 29 na watan Yunin nan, zai samu damar yin tozali da wadanda ke yi wa juna kallon hadarin kaji.

Tarayyar Turai na fuskantar matsin lamba daga Iran kan lalubo hanyar ceto yarjejeniyar nukiliya ta 2015, inda iran din ke barazanar janyewa, sai dai a farkon wannan makon Macron ya tuntube ta, yana mai ba ta baki cewa ta kara hakuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.