Macron zai ci gaba da sauye-sauye duk da tarzomar da ake yi
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai ci gaba da aiwatar a sauye-sauyen da ya fara daga lokacin da aka zabe shi, domin kuwa abubuwa ne da al’ummar kasar ke bukata, duk da cewa a daya bangaren an share tsawon watanni biyar ana gudanar da tarzomar nuna adawa da wasu daga cikin manufofinsa na siyasa a kasar.
Wallafawa ranar:
Macron wanda ke gabatar da jawabin da aka jima ana dako, a wannan alhamis ya ce manyan manufofin siyasa da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa cikin shekaru da suka gabata, sun dace da bukatun al’ummar kasar.
To sai dai shugaban ya ce a shirye yake ya yi sassaucin biyan haraji a kan Faransawa, kamar dai yadda ya dauki irin wannan alkawari a tsakiyar watan nuwambar da ya gabata.
A wani bangare na jawabinsa, shugaba Emmanuel Macorn ya bayyana nadama dangane da yadda a wasu lokuta ya kasance mai tsanantawa a matakan da yake dauka kan al’ummar kasar.
An dai share tsawon watanni biyar ana tarzoma a sassan kasar ta Faransa, inda jama’a ke nuna rashin amincewa da wasu manufofin shugaban, musamman na batutuwan da suka shafi tattalin arziki da shugaban ke dauka a cikin gida, yayin da wasu ke bayyana shi a matsayin wanda ke kokarin kare muradun attajirai da manyan kamfanonin duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu