Isa ga babban shafi
Birtaniya

Manufofin 'yan takarar Birtaniya kan Brexit

Ana ci gaba da samun banbancin ra’ayi tsakanin ‘yan takarar da ke neman maye gurbin tsohuwar Firaministar Birtaniya Theresa May dangane da shirin kasar na ficewa daga cikin kungiyar kasashen Turai.

Ra'ayin masu neman maye gurbin Theresa May ya banbanta kan ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai
Ra'ayin masu neman maye gurbin Theresa May ya banbanta kan ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai REUTERS/Hannah Mckay
Talla

Tsohon sakataren harkokin wajen kasar, Boris Johnson da ke kan gaba tsakanin ‘yan takarar, ya ce zai jinkirta biyan Euro biliyan 36 na rabuwa da EU har sai an yi wa yarjejeniyar ta Brexit kwaskwarima.

Daya 'yar takarar kuwa, Andrea Leadsom alwashi ta sha kan cewa za ta jagoranci ficewar Birtaniya  daga cikin kungiyar EU ba tare da cimma yarjejeniya ba, sannan ba tare da an kara lokacin cikar wa’adin rabuwarsu ba.

Ita kuwa Esther McVey, tsohuwar mai gabatar da shirye-shirye a kafar talabijin, cewa ta yi, a shirye take Birtaniya ta fice daga cikin EU ba tare da yarjejeniya ba, amma bayan rabuwarsu, za su iya cimma yarjejeniya kan kasuwanci.

Haka dai jumullar ‘yan takarar 11 da ke fafutukar maye gurbin Theresa May, ra’ayinsu ya banbanta, inda wasu ke shan alwashin tabbatar da yarjejeniyar da Theresa May ta cimma da EU a baya, wasu kuwa alwashin rabuwa suka yi da kungiyar babu yarjejeniya, yayinda wasu kuma ke bukatar sake bai wa ‘yan Birtaniya damar zaben raba gardama kan batun na Brexit karo na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.