Isa ga babban shafi
Birtaniya

Brexit :'Yan Majalisun Birtaniya 3 sun fice daga Jam’iyya mai mulki

A Birtaniya wasu yan Majalisun kasar guda uku da suka fito daga Jam’iyyar Konzabati mai mulkin kasar sun sanar da ficewa daga cikin ta saboda abinda suka kira matsalar da aka samu na shirin ficewa daga kungiyar Turai wanda basu gamsu da yadda ake aiwatar da shi ba.

Theresa May Firaministar Birtaniya
Theresa May Firaministar Birtaniya REUTERS/Toby Melville
Talla

Yan Majalisun uku Anna Soubry da Heidi Allen da Sarah Wollaston sun rubuta wasikar hadin gwuiwa ga Firaminista Theresa May inda suke bayyana takaicin su na daukar matakin na ficewa daga Jam’iyyar.

Yan Majalisun sun bayyana cewar zasu cigaba da zama a Majalisar tare da wasu yan Majalisu 8 da suka fice daga Jam’iyyar Leba saboda suma rashin gamsuwa da shirin ficewar daga kungiyar Turai, inda suka kafa wata kungiya ta yan baruwan mu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.