Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

May ta sake shan kaye a Majalisar Birtaniya kan Brexit

Firaministan Birtaniya Theresa May ta sake shan kaye a kuri’ar da majalisar kasar ta sake kadawa kan tsare-tsaren ficewar kasar daga EU kwanaki 43 kafin kammala ficewar kasar daga gungun kasashen Turai.

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May UK Parliament/Mark Duffy/Handout via REUTERS
Talla

Kayen wanda shi ne karo na 10 da Theresa May ke sha a gaban Majalisar kan shirin ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai EU, daga cikin ‘yan Majalisu 303 da suka kada kuri’ar 258 sun kalubalanci shirin Firaministar.

Majalisar wadda mafi rinjayen mambobinta suka kalubalanci bukatar May ta neman amincewarsu don gudanar da gyare-gyare a yarjejeniyar da ta kulla tsakaninta da shugabannin EU.

Cikin kalaman Jeremy Corbyn jagoran jam’iyyar adawa ya ce shan kayen na May alamu da ke nuna al’umma basa goyon bayan yarjejeniyar da ta cimma da EU wanda ya ce ba komi zai haifar ba, face tabarbarewar al’umura ga Birtaniyar.

Sai dai ministan kasuwanci Liam Fox ya yi gargadin illar da watsin da majalisar ta yi da yarjejeniyar ficewar kasar za ta haifar, inda ya ce akwai tantama ko majalisar ma a nan gaba za ta amince da gyare-gyaren da May ke kokarin ganin EU ta yiwa yarjejeniyar.

Shima dai sakataren shirin ficewar Keir Starmer ya zargi May da jan kafa har lokaci ya kure don ganin majalisa ta amince da yarjejeniyarta, bayan kuwa ta na sane Majalisar ba za ta yarda da kammala fita daga EU ba tare da kwakkwarar yarjejeniya ba

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.