Isa ga babban shafi
EU-Venezuela

EU ta amince da Guaido a matsayin shugaban kasar Venezuela

Majalisar Kungiyar Kasashen Turai EU ta kada kuri'ar goyon bayan jagoran 'yan adawar Venezuela Juan Guaido a matsayin sabon shugaban kasa, yayin da kuma ta bukaci ilahirin kasashen nahiyar da su goyi bayan matakin.

Juan Guaidó
Juan Guaidó Fuente: Reuters.
Talla

'Yan Majalisar Kungiyar Kasashen Turan 439 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin goyon bayan sabuwar gwamnatin jagoran ‘yan adawar, yayin da 104 suke adawa da matakin.

Majalisar ta bukaci baki dayan kasashe 27 da ke karkashin kungiyar, su amince da  Guaido a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar Venezuela har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaben shugaban kasa, karbabbe ga kowa.

A makon da ya gabata, wasu daga cikin manyan kasashen Turai suka bai wa shugaban Venezuela Nicolas Maduro wa’adin kwanaki 8, ya soke zaben watan Mayu na shekarar bara da ya ba shi damar darewa wa’adi na biyu, ya kuma shirya sabon zabe a cikin kwanaki kalilan, amma fa muddin ya saba, za su bi sawun Amurka da Brazil da Canada wajen amincewa da jagoran ‘yan adawar kasar Juan Guaido a matsayin halastaccen shugaba.

Zuwa yanzu mutane 26 suka hallaka daga cikin masu zanga-zangar adawa da shugaba Maduro  sakamakon arangama da ‘yan sanda, tun bayan soma sabuwar zanga-zangar neman kawar da shugabancinsa bayan amsa kiran jagoran ‘yan adawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.