Mexico
Rayuka sama da 70 sun salwanta a Mexico
Hukumomin kasar Mexico sun ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi lokacin dibar mai a wani bututu da ya fashe ya karu daga 66 zuwa 73.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Gwamnan Jihar Hidalgo, Omar Fayad, yace adadin ya karu ne bayan gano wasu karin gawarwaki 5, a gobarar da wasu mutane akalla 74 suka jikkata.
Wani faifan bidiyon da aka nada a wajen hadarin, ya nuna yadda mutane ke ci da wuta, yayin da wasu na gudu suna bukatar taimako.
Tuni shugaban kasa Andres Manual Lopez Obrador ya tafi yankin domin ganewa idan sa halin da ake ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu