Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na fargabar barkewar zanga-zanga mafi muni

Mahukunta a Faransa na fargabar mummunar zanga-zangar da ta fi wadda aka fuskanta a makon jiya da ma ta watannin baya, bayan da masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ke sanye da riguna dorawa ke kara farfadowa daga raunin da suka yi a karshen shekarar 2018.

Masu zanga-zanga na zargin shugaba Macron da fifita attajirai fiye da talakawa kan shirinsa na karban haraji, da kuma sauran tsare tsare da suka kunshi kara farashin man fetur.
Masu zanga-zanga na zargin shugaba Macron da fifita attajirai fiye da talakawa kan shirinsa na karban haraji, da kuma sauran tsare tsare da suka kunshi kara farashin man fetur. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Shugaban 'yan sandan Faransa Eric Morvan ya ce, akwai hasashen sake fuskantar zanga-zangar ta masu sanye da riguna dorawa masu adawa da manufofin shugaba Emmanuel Macron, wadda hasashen ke nuna cewa za ta yi muni fiye da ta baya wadda ta kai ga arangama tsakanin jami’an tsaro baya ga barnata dukiyoyi.

Ko a Asabar din makon jiya masu zanga-zangar da ake wa lakabi da yellow Vest kussan dubu hamsin suka fito a birnin Paris da wasu sassan kasar, wadda ta haura wadda aka gudanar a karshen watan Disamba, ko da dai bata kai wadda aka gani a watan Nuwamba ba, wadda ta kunshi mutane kusan dubu 300 wadanda suka barbazu a manyan titunan biranen kasar 8.

Masu zanga-zanga na zargin shugaba Macron da fifita attajirai fiye da talakawa kan shirinsa na karban haraji, da kuma sauran tsare tsare da suka kunshi kara farashin man fetur.

A bangare guda shugaban kasar Emmanuel Macron wanda a watan Disamban bara ya sanar da daukar matakin karin albashin ma'aikata baya ga janye wasu haraji da ya shirya karba ya ce yana daukar matakan ganin kawo karshen zanga-zangar ta hanyar biyan bukatun al'ummar kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.