Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

Majalisar Birtaniya za ta yi muhawara kan yarjejeniyar kasar da EU

‘Yan majalisar Birtaniya sun fara shirin tunkarar muhawarar da za su tafka, kafin kada kuri’a kan amincewa ko akasin haka, da yarjejeniyar rabuwa da kungiyar Tarayyar Turai da Firaminista Theresa May, ta cimma da kungiyar ta EU.

Dama dai Majalisar ta amince da dage batun kada kuri'ar har zuwa bayan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Dama dai Majalisar ta amince da dage batun kada kuri'ar har zuwa bayan bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara. Parliament TV handout via REUTERS
Talla

Tun cikin watan Nuwamban da ya gabata Firaminista May ta cimma yarjejeniyar da shugabannin kasashen kungiyar EU 27, sai dai wasu daga cikin ‘yan majalisar ta na kallon yarjejeniyar a matsayin wadda ka iya cutar da Birtaniya musamman ta fuskar tattalin arziki.

Zalika ‘yan Majalisar ta Birtaniya sun kuma zargi Firaministar da yin rufa-rufa kan wasu sassan yarjejeniyar kafin sanya mata hannu, musamman kan iyakokin kasar na yankin arewacin Ireland da kuma zabin yankin na ci gaba da kasancewa a karkashin hukumar shige da fice ta bai daya ta kasashen nahiyar Turan.

Theresa May dai na ci gaba da gargadin 'yan majalisun kasar kan matsalar da kasar za ta iya fuskanta matukar Majalisar ta ki amincewa da yarjejeniyar da ta dauki tsawon lokaci ta na kokarin cimmawa da EU.

Cikin watan Maris mai zuwa ne Birtaniyar za ta kammala ficewa daga EU a hukumance.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.