Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya ta damu da kwararar baki cikin kasar

Ministan Harkokin Cikin Gida na Birtaniya ya diga ayar tambaya kan yadda yawaitar masu neman mafaka ke kara tsananta musamman wadanda ke amfani da kananan kwale-kwale ta gabar ruwan Faransa zuwa Birtaniyar.

Birtaniya ta ce, ya kamata bakin-hauren su rika zama a kasar da suka fara isa a Turai
Birtaniya ta ce, ya kamata bakin-hauren su rika zama a kasar da suka fara isa a Turai CHARLY TRIBALLEAU / AFP
Talla

A ziyarar da ya kai garin Dover da ke yankin kudu maso gabashin kasar, Sajid Javid ya nuna damuwa kan yadda har yanzu Birtaniya ke samun turuwar masu neman mafaka daga Faransa.

Javid ya ce, ya gaza gamsuwa kan cewa mutanen da ke ci gaba da tururuwa zuwa Birtaniya masu neman mafaka ne, yana mai cewa idan har mafaka suke nema kamata ya yi ace sun zauna a kasar da suka fara shiga a nahiyar Turai maimakon tahowa Birtaniya.

A cewarsa, galibin masu neman mafakar kan yi amfani da gabar ruwan Faransa wajen shigowa cikin Birtaniya ta hanyar amfani da kananan kwale-kwale, bayan kuma Faransar ka iya shiga gabar Birtaniya ta fuskar bayar da kulawa ga ‘yan ciranin haka zalika ma tana da cikakken tsaro ga al’ummarta da ma baki.

Tun daga watan Oktoba ne adadin masu shigowa Birtaniyar galibi daga Iran ko Syria ke ci gaba da karuwa, in da a lokuta da dama suka fara isa Faransa kafin karasowa Birtaniya, in da rahotanni ke nuna cewa akalla mutane 539 suka tsallako Birtaniyar a 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.