Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya rattaba hannu kan umurnin janye dakarunsa daga Syria

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta tabbatar da cewa a cikin daren ranar Lahadin nan, an sanya hannu kan kudurin doka da ke bayar da umurnin fara janye dakarun kasar daga Syria kamar yadda shugaba Donald Trump ya yi alkawari.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Reuters
Talla

Trump ya ce za a janye dakarun ne lura da cewa an yi nasarar murkushe kungiyar IS a kasar, to sai dai tuni matakin ya haifar da sabani tare da marabus na sakataten tsaron kasar Jim Mattis,

Wata sanarwar da shugaba Trump ya fitar a jiya Lahadi, ta ce za a nada sabon mataimakin Mattis wato Patrick Shanahan domin maye gurbinsa a ranar 1 ga watan Janairu da ke tafe.

Turkiya dai ta yi maraba da matakin na Amurka, wanda zai ba ta damar samun karin tasiri a yakin kasar ta Syria, da kuma kokarin murkushe mayakan Kurdawa na YPG da ta ke son yi, wadanda suka taka rawa wajen yakar kungiyar ISIS a kasar tare da goyon bayan Amurka, sai dai Turkiya na kallonsu a matsayin ‘yan ta’adda kuma reshen kungiyar ‘yan tawayen PKK mai neman ballewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.