Kotu ta yi watsi da hukuncin dauri saboda taimakawa bakin-haure
Kotun daukaka kara a Faransa tayi watsi da hukuncin wata karamar kotu na daure wasu mutane biyu, saboda samun su da laifin taimakawa bakin-haure da suka shiga kasar ba tare da izini ba.
Wallafawa ranar:
Da fari dai karamar kotun ta daure Cedric Herrou, wani manomi tsawon watanni 4 a gidan yari saboda taimakawa wasu baki 150 da suka shiga Faransa daga Italia, tare da wasu ‘yan kasar Eritrea 50 da ya baiwa mafaka.
Shi kuwa Pierre-Alain Mannoni an daure shi ne watanni biyu a gidan yari.
Alkalin kotun daukaka karar yace hukuncin ya sabawa halayyar Faransawa na taimakawa baki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu