Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya dakatar da baiwa 'yan gudun hijira damar shiga Amurka

Shugaba Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta dakatar da shigar ‘yan gudun hijira cikin Amurka daga kan iyakar ta da Mexico na tsawon kwanaki 90.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Sai dai dokar bata shafi kananan yaran da basu iso kasar ta Amurka da Iyayensu ba.

Sai dai ana sa ran kungiyoyin kare hakkin dan adam zasu kalubalanci wannan doka a kotun, bayan da suka bayyanata a matsayin matakin da y a sabawa kundin tsarin mulkin Amurka da ma dokokin kasa da kasa.

A halin da ake ciki dai Amurka ta girke sojoji akalla 5,000 a kan iyakarta da Mexico, domin hana tawagar ‘yan gudun hijira mai dauke da kimanin mutane 7000 shiga Amurka, wadanda suka taso daga kasashen nahiyar kudanci da tsakiyar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.