Isa ga babban shafi
Spain

A Spain, jam'iyyar PP ta zabi Pablo Casado a matsayin sabon shugaba

Jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya ta PP a kasar Spain ta zabi Pablo Casado mai shekaru 37 a duniya a matsayin sabon shugabanta, inda zai maye gurbin tsohon Firaminista Mariano Rajoy da aka tsige daga mukaminsa cikin watan yunin da ya gabata.

Pablo Casado, sabon shugaban jam'iyyar PP a Spain
Pablo Casado, sabon shugaban jam'iyyar PP a Spain PIERRE-PHILIPPE MARCOU / AFP
Talla

Casado ya yi nasarar doke abokiyar hamayyarsa Soraya Saenz de Santamaria, wadda tuni ta amince da shan kaye tare da yin alkawarin cewa za ta yi masa biyayya.

Sabon shugaban jam’iyyar mutum ne mai adawa da wasu manufofi, cikin har da zubar da cikin, auren jinsi, tare da alkawarin cewa zai yi riko da koyarwar cocin katolika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.