Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai zaftare kudaden da gwamnati ke kashewa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce nan da wani gajeren lokaci, gwamnatinsa za ta zaftare kudaden da ta ke kashewa wajen gudanar wasu muhimman ma’aikatun ta.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, yayin gabatar da jawabi ga 'yan majalisun kasar. Ranar 9 ga watan Yuli, 2018.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, yayin gabatar da jawabi ga 'yan majalisun kasar. Ranar 9 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Shugaba Macron ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan majalisun kasar a fadar birnin Versailles, inda ya gabatar musu da jawabi na tsawon sa’a guda, akan shirin yin garambawul ga tsarin tafiyar da muhimman ma’aikatu da kuma hukumomin kasar.

A wannan makon ne ‘yan majalisun Faransa za su soma muhawara akan kudurin da ya mika musu, na neman yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, wanda a karkashinsa za’a rage yawan ‘yan majalisun wakilai da na dattijan kasar da akalla kasha daya bisa uku.

Zalika kudurin ya na neman bai wa ‘yan jaridu damar bayyana abin da ke wakana a majalisun kasar kai tsaye ya yin da suke zama.

Tuni dai shugaba Emmanuel Macron ya soma fuskantar turjiya daga wasu kungiyoyin kwadagon kasar, sakamakon daukar matakin gudanar da wasu sauye-sauye ga dokokin kwadago, da suka shafi jami’o’in kasar da kuma Kamfanin sufurin jiragen kasa mallakar kasar na SNCF.

A farkon watan Afrilu da ya gabata na wannan shekara ta 2018, ma'aikatan jiragen kasa a Faransa suka fara yajin aikin watanni uku don ci gaba da  matsin lamba ga shugaba Emmanuel Macron don ganin ya dakatar da aiwatar da shirinsa na sauye sauye.

Yajin aikin da Kungiyar Ma’aikatan Jiragen kasa ta kira ta ce, ba zai tsaya ba har sai shugaba Emmanuel Macron ya janye aniyarsa ta yi wa bangaren sufurin garambawul.

A karkashin tsarin yajin aikin, ma’aikatan za su rika dakatar da sufurin ne sau biyu daga cikin kwanaki 5 na aiki, wanda hakan zai jefa matafiya miliyan hudu da rabi cikin kunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.