Isa ga babban shafi
Rasha

Putin ya karbi rantsuwar shugabancin Rasha wa'adi na hudu

An rantsar da Vladmir Putin a matsayin shugaban Rasha wa’adi na hudu, wanda acikinsa zai sake shafe shekaru 6 yana jagorantar kasar.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Sergei Ilnitsky/Pool via REUTERS
Talla

An gudanar da bikin rantsuwar a fadar Grand Kremlin da ke babban birnin kasar Moscow, shekaru 18 kenan tun bayanda Putin mai shekaru 65 ya fara shugabancin kasar.

A watan Maris da ya gabata ne Putin ya lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana, inda ya lashe kashi 76% na kuri’un da aka kada.

Dan takara daga jam’iyyar Communist Pavel Grudinin ne ya zo na biyu a zaben da kuri’u kashi 11, yayinda Vladmir Zhirinovsky ya ke biye da su da kashi 5 na kuri’un da aka kada.

A ranar Asabar wasu dubban ‘yan kasar ta Rasha suka gudanar da zanga-zanga a manyan biranen kasar akalla 90, domin amsa kiran jagoran ‘yan adawar kasar Alexey Navalny, da yayi watsi da sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar.

Har yanzu dai ‘yan adawa kusan 1,600 ne ke tsare a hannun jami’an tsaron kasar ta Rasha, bisa samunsu da laifin tayar da tarzoma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.