Isa ga babban shafi
Faransa

An ci gaba da sauraren shari’a Jerome Cahuzac a Faransa

An fara sauraren shari’ar da tsohon ministan kasafin kudin Faransa, Jarome Cahuzac, ya daukaka kan hukuncin da aka zartar masa na daurin shekaru uku a gidan yari, bayanda aka kama shi da laifin boye dukiya don kaucewa biyan haraji.Badakalar da ake gani da mafi muni cikin mukarraban gwamnatin tsohon shugaban kasar Francoise Hollande.

Tsohon Ministan kasafin kudin faransa da ke fuskantar shari'ar boye kudi don kaucewa biyan haraji, badakalar da ake kallo mafi muni zamanin mulkin Francoise Hollande.
Tsohon Ministan kasafin kudin faransa da ke fuskantar shari'ar boye kudi don kaucewa biyan haraji, badakalar da ake kallo mafi muni zamanin mulkin Francoise Hollande. rfi
Talla

Cikin shekara ta 2013 ne Mr Cahuzac ya ajiye aikin sa bayanda ya zamo wata silar abun kunya ga tsohuwar gwamnatin Hollande, lokacin da aka gano cewar yana boye da tarin kudade don gudun biyan haraji.

A 2016 ne dai aka kamashi dumu dumu da laifin boye dukiya mai tarin yawa a wani asusun ajiya a bankin swiss daga kamfanin sa na dashen gashi da suke gudanarwa tare da tsohuwar matarsa.

Mr Cahuzac mai shekaru 65 da ke neman kotu ta sauya hukuncin da aka yanke masa tun da farko na shafe shekaru 3 a gidan yari matukar dai bai samu nasara ba hukuncin zai koma daurin shekaru biyar a gidan yari tare da biyan tarar Yuro dubu dari uku da saba’in da biyar.

A bangare guda kuma Kotun ta yankewa mai dakinsa Patricia Menard hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari sakamakon taimakawa wajen aikata laifin boye tarin kudin.

Haka zalika kotun ta kuma haramtawa Mr Cahuzac shiga duk wasu al'amuran siyasa har karshen rayuwarsa, bayan da ya kafa hujjar boye kudin gaban kotun da cewa yana gujewa kada iyalansa su fuskanci tagayyara ne, wadanda ya ce tun da farko sun saba da rayuwa a cikin daula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.