Merkel na tattaunawa da 'yan adawar siyasa
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara tattaunawa da shugaban jam’iyyar adawa ta Social Democrats SDP, Martin Schulz, domin kawo karshen halin rashin tabbas da siyasar kasar ta Jamus ta tsinci kanta.
Wallafawa ranar:
Bayan zaben Jamus na watan Satumba da Merkel ta gaza samun rinjayen da take bukata na kafa gwamnati, jam'iyyar adawa ta SPD ta ce ba za ta sabunta kawance kafa gwamnati da Merkel din ba.
Sai dai bayan rushewar kokarin Angela Merkel na samun hadin kan sauran jam’iyyun adawa na FDP da Greens a farkon wannan watan, jam’iyyar SPD ta Martin Schulz ta fuskanci karin matsin lamba daga shugabanni dama sauran ‘yan kasar ta Jamus kan ta amince da sabunta kawancenta da gwamnatin Merkel.
Angela Merkel ita ce shugabar jam’iyya mai mulkin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu