Isa ga babban shafi
Jamus

Merkel za ta yi zawarcin ‘yan Jam’iyarta

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta yi kokarin shawo kan ‘ya’yan Jam’iyyarta da suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar ‘yan ra’ayin rikau, yayin da ta fara tuntubar wasu jam’iyyu domin kafa sabuwar gwamnati.

Angela Merkel Shugabar gwamnatin Jamus
Angela Merkel Shugabar gwamnatin Jamus REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Sakamakon zaben da aka yi a karshen mako wanda tuni ya ba Angela Merkel nasara, ya kuma ba Jam’iyyar da ke kyamar baki da addinin Islama nasara ta farko, wanda hakan ke nuna cewar ‘ya’yan Jam’iyyar Merkel miliyan guda ne suka sauya sheka.

Merkel ta ce fatar su ta samun gagarumar nasara ta dushe, irinsa na farko tun shekarar 1949, ganin yadda hadin kan Jam’iyyun CDU da CSU suka samu kashi 33.

Merkel mai shekaru 63 ta ce za ta fara tattaunawar kafa sabuwar gwamnati da wasu kananan jam’iyyu biyu, bayan Jam’iyyar Social Democrat da suka kwashe shekaru 8 suna aiki tare.

Tuni Social Democrat ta ce ba za ta shiga gwamnatin ta Merkel ba, domin za ta koma bangaren adawa.

Jaridar Der Spiegel ta zargi Merkel ta bijirewar da wasu ‘ya’yan jam’iyyarta suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.