Isa ga babban shafi
Spain-Calatonia

Spain ta ki hawa teburin sulhu da Catalonia

Gwamantin Spain ta ce ba za ta amince da shiga tsakanin wata kasa domin warware sabanin da ke tsakaninta da Catalonia matukatar dai mahukuntan yankin ba su dawo daga rakiyar batun ballewa ba.

Firaministan Spain Mariano Rajoy
Firaministan Spain Mariano Rajoy REUTERS/Albert Gea
Talla

Wata majiya a kusa da shugabannin masu fafutukar ballewar, ta bayyana cewa nan zuwa lokaci kadan ne za su sanar da ‘yancin kan yankin a hukumance, abinda kuma gwamnatin Spain ta kira haramtacce.

Wannan shi ne rikicin siyasa mafi girma da Spain ta taba fuskanta a shekaru masu yawa.

Firaministan Spain Mariano Rajoy ya bukaci shugabannin Catalonia su bi tsarin doka, a yayin da suke shirin sanar da samun ‘yancin kai.

A ranar Litinin mai zuwa ake sa ran shugabannin Catalonia za su ayyana ‘yancin kai a majalisar yankin.

Amma kotun kundin tsarin Spain ta bukaci su dakatar da matakin har sai ta saurari karar da ‘yan adawar yankin suka shigar a gabanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.