Isa ga babban shafi
Faransa

Jam'iyyar Socialist ta sanya shalkwatanta a kasuwa

Shugabannin jam’iyyar Socialist ta Faransa sun sanar da shirinsu na sanya ginin shalkwatan jam’iyyar a kasuwa, wanda rahotanni ke cewa, za a siyar da shi tsakanin Euro miliyan 40 zuwa miliyan 70.

Ginin shalkwatan jam'iyyar Socialist da ke  Rue de Solférino a birnin Paris na Faransa
Ginin shalkwatan jam'iyyar Socialist da ke Rue de Solférino a birnin Paris na Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Ma’ajin jam’iyyar Jean Francois Debat ya ce, daukan matakin na da matukar wahala, amma ya ce, dole ne su yi haka saboda matsalar kudi da jam’iyyar ke fama da ita.

Kazalika, matakin zai bai wa ‘ya‘yan jam’iyyar damar tinkarar makomar siyasarsu a Faransa kamar yadda Debat ya shaida wa manema labarai a birnin Paris.

Wannan dai na zuwa ne bayan mummunan kayin da Jam’iyyar ta sha a zaben shugabancin kasar da na ‘yan majalisu da aka gudanar a cikin watannin Mayu da Junin da suka gabata.

Jam’iyyar Socialist ta tsohon shugaban kasar Francois Hollande, ta rasa kujeru sama da 250 a zaben na ‘yan Majalisu, yayin da jamiyyar Emmanuel Macron ta Republican on the move ta samu gagarumin rinjaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.