Isa ga babban shafi
Turai

Guguwar Maria ta yi mummunar barna a Dominica

Firaministan Dominica Roosevelt Skerrit, yace mahaukaciyar guguwar Maria da ta afkawa tsibirin, ta lalata duk wani abinda kudi ke iya saye.

Yankin Tsibirin Guadeloupe na Faransa yayinda guguwar Maria ke tunkararsa.
Yankin Tsibirin Guadeloupe na Faransa yayinda guguwar Maria ke tunkararsa. REUTERS/Andres Martinez Casares
Talla

Skerrit, yace guguwar ta dauke daukacin rufin gidajen dake tsibirin, kamar yadda mutanen da yayi magana da su suka shaida masa.

Firaministan ya bukaci taimakon kasashen duniya domin kaiwa jama’arsa dauki.

A yau Talata guguwar Maria da karfinta ya kai mataki na 5 ta aukawa Dominica da gudun kilomita 257 a sa’a guda.

Gugwar ta Maria na bin sawun ta Irma ne wadda har yanzu yankunan Carribea basu kammala murmurewa daga bala’inta ba.

A halin yanzu shugaban dake mulkin tsibirin Guadeloupe a yankin Caribbean ya bukaci kwashe mutanen dake fuskantar hadari daga guguwar Maria da yanzu haka ta dumfari yankin.

Sanarwar da ya bayar ta bukaci rufe daukacin yankunan da ake zaton suna fuskantar hadari domin kare lafiyar jama’a.

Shi ma dai tsibirin Guadeloupe dake karkshin ikon Faransa ya fuskanci hadari sakamakon guguwar Irma da aka samu makwanni biyu da suka wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.