Mutane 400,000 Suka Shiga Zanga-Zanga A Faransa
Mutane da suka kai dubu dari biyu da ashirin da uku suka shiga zanga-zangan gamagari da aka yi a fadin kasar Faransa yau Talata domin nuna adawa da sauye-sauyen tsarin Kodago, wanda shine karo na farko da Shugaba Emmanuel Macron ke fuskanta.
Wallafawa ranar:
Sai dai kuma ita babbar Kungiyar Kodago ta Faransa CGT ta bayyana cewa mutane akalla dubu dari hudu suka shiga jerin gwanon da suka kira, kuma an yi cikin kwanciyar hankali.
Shugaban Kungiyar Phillippe Martinez ya bayyana cewa bukatar su ta biya.
Wasu alkaluman na cewa mutane dubu ashirin da biyar suka shiga jerin gwano da aka yi a Paris, yayin da a birnin Marseille mutane dubu bakwai da dari biyar suka shiga .
Ma’aikatar Harkokin cikin gida ta Faransa ta bayyana cewa mutane 13 suna tsare hannun jami’an tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu