Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikata sun sanya kafar wando daya da gwamnatin Faransa

Kungiyoyin kwadago a Faransa, sun shirya yajin aiki da kuma gudanar da zanga zanga don nuna adawa ga shirin sauyin dokar kwadago na shugaba Emmanuel Macron.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Yunkurin dai zai zama zakaran gwajin dafi ga sabuwar gwamnatin Faransa, kasancewar itace ta farko da kungiyoyin kwadagon suka kira.

Daga cikin jerin matakan garambawul din da Macron ya shirya aiwatarwa a dokar kwadagon kasar, akwai bai wa shugabannin kamfanoni karfin dauka da korar ma’aikata dai dai da tsarinsu.

Sai dai kuma daga cikin manyan kungiyoyin kwadagon kasar guda uku dake adawa da shirin Macron, kungiyoyin FO da CFDT sun bayyana shirin su na kauracewa yajin aikin.

Ita kuwa kungiyar CGT mafi girma a kasar, tace ya zama wajibi ta gudanar da yajin aikin da kuma gangami domin nuna rashin amincewar ta da shirin.

Daya daga cikin .yan takaran shugaban kasa a zaben da ya gabata a Faransa, Jean-Luc Melenchon, ya goyi bayan shirin shiga zanga zangar saboda abinda ya kira juyin mulki ga ma’aikata, inda ya kira wani yajin aikin na dabam ranar 23 ga watan Satumba 2017.

Sakatare Janar na kungiyar CGT Philippe Martinez yace an ware wurare 180 da za’a gudanar da gangami a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.